30 Maris 2021 - 18:03
Zarif: Ta Hanyar Tattaunawa Ne Kadai Za A Iya Samun Zaman Lafiya A Kasar Afghansitan

Ministan harkokin wajen na Iran Muhammad Jawad Zarif wanda yake halartar taron kasashen tsakiyar Asiya da ake yi a kasar Tajikistan ya bayyana cewa; Tattaunawa ce kadai hanyar tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Afghansitan.”

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da cewa; “Duk wata tattaunawa da za a yi domin samo hanyar zaman lafiya, to wajibi ne ta kunshi bai wa a’ummar Afghansitan hakkin ayyana makomarsu.”

Har ila yau Muhammad Jawad Zarif ya yi kira ga MDD da ta zama mai daukar matakin da zai taimaka wajen yin tattaunawar cikin sauki da kuma yin watsi da duk wata matsaya da za a yi kokarin tilasta wa al’ummar kasar daga waje.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma jinjinawa al’ummar Afghanistan da ya yi nasarar kafa gwamnati mai aiki da doka, musamman bayan nasarar da aka samu ta rubuta wa kasar sabon tsarin mulki.

342/